Boma-Bomai Uku sun Tashi a Maiduguri

Tashin Boma-Bomai

A yau an samu tashin wasu boma-bamai uku a wurare daban-daban a cikin birnin Maduguri, wanda yayi sandiyar mutuwar mutane da dama da kuma raunta wasu.

Boma din farko ya tashi ne a wani yankin a tashar Baga, inda ake saye da sayarwa da kuma cinkoson jama’a, wanda ya jefa jama’a dake gudanar da harkokin cinikayya cikin halin damuwa.

Awa daya bayan tashin Bom din sai wani Bom din kuma ya sake tashi a daf da kasuwar Litinin inda ake saton wani dan kunar bakin wake ne ya kai harin.

Bom, na uku kuwa ya tashi ne a tashar motar Borno, Express, daya daga cikin mayan tashohin dake hada-hadar jigilar fasinjoji, masu dogon zango.

A yanzu haka babban asibitin dake cikin garin Maiduguri, na da gawarwakin mutane talatin da shida wanda mafi yawansu mata ne da majiyata fiye da saba’in, wadanda duk an kwaso sune daga tashar Baga.

Kwamishinar ma’aikatar sharia na jihar Borno Barrister Kaka Shehu Lawal, ya tabbatar, da afkuwar lamarin, da kuma ummartan asibitocin suyi wa jama’ar, da suka jirkita magani kyauta.