Burtaniya Zata Hana Shiga Jirgin Sama Da Kwamfutar Hannu

Kasar Burtaniya ta fadi jiya Talata cewa za ta hana matafiya shigowa da kananan kamfutocin da akan aje kan cinya da sauran kayan lataroni masu dan girma, muddun sun fito ne daga wasu kasashe 6 na Gabas Ta Tsakiya, bayan mataki makamancin wannan da Amurka ta dauka.

Sabon umurnin na Burtaniya zai haramta shigowa da duk wani kayan lataroni mai tsawon santimita 16, da fadin santimita 9 da kuma kaurin santimita 1.5 a duk wani jirgin saman da ya fito daga kasar Turkiyya, da Labanon da Jordan da Masar da Tunisiya da kuma Saudiyya.

Tun da farko a ranar Talata, Hukumar Tabbatar da lafiyar Matafiya ta Amurka ta bayar da umurni makamancin wannan ga matafiya a jiragen saman da kan taho daga wasu filayen jiragen sama 10 na Gabas Ta Tsakiya.