Dan Taxi Ya Tona Asirin Wata Barauniya

Wasu rahotannin da 'yan sandan kasar Amurka suka fitar a garin Rochester sun bayyana yadda wata yarinya 'yar shekaru ashirin da biyu ta ba wasu masu sayar da kaya mamaki.

Kamar yadda hukumomi suka bayyana, wani dan tasi ne ya taimakawa jami'an tsaron 'yan sanda cafke wannan yarinya a yayin da ya ji irin bayanai da kuma yadda aka fadi suffar wannan yarinya.

Jami'in 'yan sandan mai suna Jim Evenson ya fada wa mujallar post-Bulletin cewar, wannan yarinyar ta shiga wani babban shago ne kamar zata yi sayayya daga nan sai ta fakaici idanun masu sayar da kayan tai wuf! ta kwashi kudi har dalar Amurka dari uku, ta kuma kada jami'in tsaron da ya yi kokarin cafketa sannan ta zura da gudu.

Ana cikin neman yarinyar ne sai kwatsam wannan dan tasi ya ce "kai amma yanzu yanzu na kai wata yarinya wani Otal mai suna Kahler Grand Hotel kuma ta yi kama da wadda kuka fadi kamanninta. Sai kawai 'yan sandan suka bi shi zuwa Otal din inda suka cafke wannan yarinya 'yar shekaru ashirin da biyu mai halin bera.