Diego Simeone Ya Kara Kwantirakinsa A Atletico Madrid

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, na kasar Spain, Diego Simeone, ya sake tsawaita kwantirakinsa da kungiyar na tsawon shekaru biyu, inda zai karkare a shekara ta 2020.

Simeone, dan shekaru arba'in da bakwai (47) da haihuwa dan kasar Argentina, ya kasance cikin jerin sunayen masu horas da 'yan wasa da sukafi dadi a lig din kasar Spain, inda ya fara aiki da kungiyar a shekara 2011 yazuwa yanzu, kimanin shekaru shida kenan, Kuma tsohon dan wasan kungiyar ta Atletico Madrid ne,

Diego ya sami nasarori da dama a kungiyar a matsayinsa na mai horaswa, cikin nasarorin nasa da ya samu sun hada da lashe kofin Lig wato Laliga na kasar Spain, a shekara 2014,

Bayan haka Diego Simenon, ya kai kungiyar ta Atletico, zuwa wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar turai (UCL) har sau biyu a 2014 da kuma 2016, sai dai bai samu nasarar lashe kofin koda sau daya ba.

A shekara ta dubu biyu da sha biyu 2012, Simeone ya samu nasarar daukar kofin (Europe League,) sai kuma a shekara ta dubu biyu da sha uku da ya lashe gasar (Spanish Super Cup,) a nan kasar Spain.

Kungiyar ta Atletico Madrid, a bana dai ta fara wasan laliga ne da kungiyar Girona, inda suka tashi 2-2 sai kuma ta lallasa Las Palmas, daci biyar da daya 5-1 a wasan mako na biyu na laliga 2017/18.

Your browser doesn’t support HTML5

Diego Simeone Ya Kara Kwantirakinsa A Atletico Madrid