Manajan Chelsea, Jose Mourinho, ya ce bashi ke da alhakin sayo dan wasa Papy Djilobodji ba.
Dan wasan bayan na Senegal ya isa Stamford Bridge ne a daidai ranar cikar wa’adin rufe kasuwar sayen ‘yan wasa.
Rahotanni sun ce an saye shi a farashin kudi Pam miliyan 4, bayan da Chelsea ta gaza siyan dan wasan Everton John Stones.
“Djilobodji ba zabi na ba ne,” Mourinho ya ce a yau juma’a, a wani taron manema labarai.
“Zabin wani ne da na amincewa, duk abu daya ne.” In ji Mourinho.
Manajan na Chelsea ya kara da cewa, “wanda ya ce min Djilobodji zai kasance kwararren dan wasa a tawagarmu, shi ne ya ce min Kurt Zouma zai kasance hakan.”
Mourinho ya ce ba za su kasance masu sa’a ba, idan har Djilobodji zai zamanto suna bukatarsa a tawagar su.