A Hukumance, an bude gasar wasannin Olympics a yau a Birnin Pyeonchang da ke Korea ta Kudu.
Masu sha’awar wasannin, sun nuna dauriya, inda suka fita duk da sanyin da ake fama da shi, domin su kalli wasannin wuta da aka yi, da kuma faretin tawagogin ‘yan wasan da za su kara, yayin da suke shiga filin wasan.
Babu tantama, masu lura da al’amura sun ce wasannin na Olympics, zasu zo da abubuwan ja hankali, inda ake ganin hadin kan da Korea ta Arewa da makwabciyarta ta Kudu, zai kasance babban lamari.
A daya bangaren kuma, da safiyar yau Juma’a mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence, ya isa Birnin na Pyeonchang domin halartar wasannin bude gasar, inda ya gana da ‘yan Korea ta Arewa da suka bijirewa gwamnati suka sauya sheka.
Jami’an Amurka, sun ce babu yiwuwar Mataikamin shugaban kasar na Amurka zai gana da jami’an Korea ta Arewa a wajen wasannin na Olympics. Ita ma kafar yada labaran Korea ta Arewa a ranar Alhamis, ta ruwaito cewa, babu wata alama da ke nuna cewa jami’an Korea ta Arewan za su nemi a gana.
Wannan na faruwa ne yayin da ‘yar uwar shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un ta isa Korea ta Kudu domin halartar gasar. Ita ce ta farko ciki iyalan da suka dade suna mulkin kasar ta Koraea ta Arewa, da ta ziyarci Korea ta Kudu, tun bayan karshen yakin Korea da aka yi daga shekarar 1950 zuwa da 53.