Kungiyar kwallon kafar matasan Najeriya ta Flying Eagles ta samu nasarar shiga gasar cin kofin duniya na matasa ‘yan kasa da shekaru ashirin, na hukumar FIFA, hakan ya biyo bayan lallasa kasar Kongo 4-1 kuma shine karo na biyu da matasan suka sami nasara a wasan da ake yi a kasar Sanigal.
Najeriya ta baiwa Sanigal kashi daci 3-1 a wasan su na farko da aka yi a ranar Lahadin data wuce. Da wannan nasarar dai Najeriyar ta samu damar zuwa wasan kusa da karshe na cin kofin matsan Afirka, da kuma shiga gasar cin kofin duniya na matasa, kuma ita ke kan gaba a rukunin A da maki shida.
Ifeanyi Matthew ya fara kafa wa Najeriya harsashen samun nasara alokacin da ya jefa kwallon farko minti biyar da fara wasan, Kaftin din matasan Musa Mohammed ne ya zarga kwallo ta biyu cikin mintuna talatin da shida, bayan da Taiwo Awoniyi ya fadi. Musa ne dai ya kara jefa kwallo ta uku cikin mintuna goma da dawowa daga hutun rabin lokaci, bayan haka ne Silvere Ganvoula Mboussy ya jefa kwallo daya.
Awoniyi ne ya jefa kwallo ta hudu a cikin mintuna tamanin da takwas na wasan. A halin da ake ciki an fitar da ‘dan wasan Kongo Georges Kader Bidimbou daga gasar.
‘Dan wasan mai shekaru goma sha tara da haihuwa ya yi targade, kuma zai samu warkewa ba a kan lokaci ya dawo wasan da za’a gama a ranar Lahadi ashirin da biyu ga watan Maris na wannan shekarar da muke ciki.