Gwamnan Bauchi ya bayyana yadda zai yi anfani da tallafin kudi daga Amurka

Jihar Bauchi

A firar da ya yi da Muryar Amurka a nan Washington DC gwamnan Bauchi Barrister M. A. Abubakar ya bayyana yada zai yi anfani da tallafin kudi na miliyan 58 daga Amurka domin inganta harkokin ilimi a jihar

Yayinda yake zantawa da Muryar Amurka gwamnan jihar Bauchi Barrister M.A.Abubakar yace zasu yi anfani da tallafin kudin daga Amurka wajen inganta yadda ake tafiyar da harkokin ilimi a jihar

Jihar zata yi anfai da tallafin wajen wani shiri na musamman na agazawa 'yan asalin jihar daga kauyuka musamman wadanda suke fama da talauci. A karkashin shirin zasu zakulo gidajen da suka fi talauci a dinga basu nera dubu biyar biyar kowane wata domin ya taimakawa rayuwarsu a kuma kara masu kaimi wajen tura 'ya'yansu zuwa makarantu musamman 'ya'ya mata.

Ita ma jihar zata saka nata kason cikin tallafin da Amurka ta bayar na dalar Amurka miliyan hamsin da takwas.

Banda saka 'ya'yansu makaranta shirin bada kudin zai taimaka masu su dinga kai 'ya'yan asibiti idan bukatar yin hakan ta taso. Sabo da tsananin talauci akwai mutanen da ko tunkarar asibiti basa yi. Wasu basu da kudin da zasu biya abun hawa ya kaisu inda asibiti yake.

Akwai kuma shirin horas da masu hannu da shuni da malaman makarantu yadda ake koyaswa domin su koyi hanyoyi na zamani na gudanar da harkokin ilimi.

Ga karin bayani.