Gwamnatin Obama Na Shirin Bullo Da Sharuddan Amfani Da Motoci Masu Sarrafa Kansu

Idan komi ya tafi kamar yadda aka tsara, nan da shekara daya da watanni, wasu dalibai a jami'ar Cornell dake nan Amurka zasu tura tauraron adam zuwa sararin subahana wanda zai yi aiki da ruwa. Tauroron zaiyi shawagi kusa da duniyar wata.

Tawagar daliban zasu tura taurarin dan adam din biyu kafada da kafada, a zaman wani bangare na kasar da hukumar binciken sararin samaniyar Amurka ta shirya domin dalibai na ganin wadanda zasu iya kera kananan taurarin dan'Adam da zasu iya gudanar bincike a sararin subahana.

A halinda ake ciki kuma,gwamnatin Obama tana shirin bullo da sharuddan yadda motoci da basu da matuka zasu yi aiki, a dai dai lokcinda jihohi suke aiki wajen kafa dokokin yada matuka zasu yi amfani da kara kan hanyoyi.