Hakan ya Zama Wajibi Saboda Yarfe da Cin Zarafin Kannywood

Falalu Dorayi Kannywood

Wani jigo mai shirya Fina Finai, a Kungiyar masu Fina Finai ta Kannywood, Falalu Dorayi, ya bayana cewar babu wani mai shirya Fina Finai ko gabatarwa da zai iya daukar mai sha’awar shiga wasa kai tsaye.

Ya bayana haka ne ga wakiliyar Dandalin Voa Baraka Bashir, a wani hira da suka yi a birnin Kano.

Ya kara da cewa daukan ‘yan wasa alhaki ne na kungiya, kuma yace kungiyar tana bin ka’idoji, kamar sanin mahaifan masu bukatar shiga wasa, kungiyar tafi yadda da yayye maza sun yiwa mai bukatar shiga wasa jagora domin sun suka fi zafi a gida.

Yana mai cewa hakan ya zama wajibi saboda yarfe da cin zarafi yasa kungiyar ta fito da wannan tsari tun shekarar 2005, yace an kama yara da suka zo shiga wasan Fina Finai batare da izini iyayen su ba wanda da bisa bayan an maida su gida iyayen sukan kasance masu yiwa ‘yan kungiyar gidiya.
Maida yaran ga iyayen su idan har sun zo bada sanin iyayen su ba shine mafi a’ala ga kungiyar.