Har Yanzu ba Wani Abin da ya Biyo Baya

Dandali ya sami zantawa da wani matashi likita kuma mai sana’ar kiwon kaji, yace ya share shekaru biyar yana wanan sana’a. A wata hira da wakiliyar sashin Hausa na muryar Amurka Baraka Bashir tayi dashi, yayi bayani musamman a game da abin da ya ja ra’ayinsa a kan wannan sana’a da kuma kalu balen da ya fuskanta.

Matashin mai suna Aliyu Mustapha dai yace shi ma’aikaci ne kuma ya yi shi’awar sana’ar kiwon kajin ne musamman yadda yaga sauran matasa da ‘yan uwa marasa karfi kwarai nayin wannan sana’a, shi kuma sai ya gwada tunda yana da hali.

A cewar sa ya fara da kaji har guda dubu shidda ne, ya kuma dauki ma’aikata mutum shidda wadanda suke kula da kajin da kuma basu abinci. “muna sayar da kwai, da kajin kai harma da kashin kajin muna sayar wa” inji Aliyu Mustapha, babu abin da suke zubarwa domin komi na da amfani a wurin jama’a da sauran manoma.

Daga karshe yayi Magana akan irin kalubalen da suka fuskanta wanda a cewar shi da kamar siyasa cikin al’amarin, domin an kashe kajin nashi duka domin gudun yaduwar cutar murar tsintsaye kuma har yanzu ba wani abin da ya biyo baya, ko diyyar kajin ma ba’a basuba amma suna sa ran hakan kila ta yiwu.