Yanzu haka ‘yan wasan kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars, guda biyar suna Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, bayan da ‘yan fashi suka harbe su akan hanyar Abaji zuwa Lakoja ranar Alhamis din data gabata, yayin da suke hanyar zuwa Owerri a can jihar Imo domin gudanar da wasan gasar kwararrun ‘yan wasan Najeriya.
Daya daga cikin taurarin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Gambo Mohammed yace, “Dole mu godewa Allah daya barmu muka tsira da ranmu, yadda mutanen nan suka zo sunzone su kashe wasu a cikin mu, soboda ni wanda ya harbe gaba da gaba ya harbe ni.”
Shima daya daga cikin ‘yan wasan da ‘yan fashin suka harba Murtala Adamu, na ganin yadda mutanen suka tunkaro su tabbas basuyi tunanin abin zai tsaya a haka ba, amma cikin ikon Allah abin yazo da sauki kasancewar babu wanda yarasa ransa a wannan hari.
Baya ga Gambo Mohammed da Murtala Adamu, maharban sun habi Moses Ekpai da Eneji Otekpa dakuma Rueben Ogbonnaya, jami’in lafiya dake tare da ‘yan kungiyar ta Kano Pillars Muntari Sani, yayi karin haske kan yadda al’amarin ya faru inda ya shaida mana cewa alokacin da suka tsaya maharan dauke da bindigogi kuma suka fara harbi suna tambayar kudade da wayoyin hannu, wanda duk aka mika musu amma duk da haka suka rinka harbi cikin motar.
Jami’in labarun hukumar kungiyar Kano Pillars, Lurwanu Idris ya bada fadawa wakilin mu Muhmud Kwari cewa sunyi duk abin da yakamata daga kowanne bangare sun tuntubi hukumomin tsaro kamar rundunar ‘yan sanda ta birnin tarayya da ta jihar Kogi, kasancewar a yankin sune wannan abu ya faru, kuma sun tabbatar da cewa suna nan suna cigaba da bincike domin zakulo duk wani mai ruwa da tsaki kan wannan hari.