Hukumar NFF Ta Gargadi Kungiyar Golden Eaglet

Golden Eaglets U-17

Hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta shimfida dokokin aiki ga duk ma’aikata da matasan kungiyar Golden Eaglet.

Kamar yadda hukumar ta fitar a shafinta na yanar gizo, tace tana tsammanin duk ‘yan wasan Najeriya zasu ‘dauki kansu da mutunci a filin wasa ko ba’a filin wasa ba.

Shima mai kula harkokin kungiyar Eaglet Price Udofia, yace suma sauran ma’aikatan Golden Eaglet suna kan tafarkin dokokin da hukumar kwallon kafar Najeriya ta shimfida, kuma bazasu bijire mata ba wajen aikata wasu abubuwa da hukumar ta haramta, haka suma ‘yan wasa an tabbatar musu da cewa bin tsarin ka’idojin hukumar ba abin wasa bane.

Udofia ya kuma ce baki ‘daya ‘yan wasa da jami’an kungiyar dole ne su bi doka da oda.

Tuntuni dai ‘yan wasan suka fara wasannin horasawa a filin wasan Karkanda dake jihar Katsina, karkashin kulawar babban koch Emmanuel Amuneke.

Koch Amuneke dai yace, “munzo nan domin yin abinda ya kawo mu, kuma dole ne mutum ya nuna bajintarsa da kare mutuncin sa saboda ‘yan wasa 21 ne kadai za’a zaba domin zuwa wasan cin kofin duniya a kasar chile.”