Hukumar dake kula da wasannin kwallon kafa ta tarayyan Najeriya, (NFF) ta tsaida ranar Alhamis, 19/10/2017 a matsayin ranar da zata gudanar da babban taronta na shekara shekara.
Haka kuma hukumar ta NFF tace za'ayi taron ne a garin Jos, ta jihar Plateau, bayan an buga wasan da Najeriya, zatayi da kasar Zambia, ranar Asabar 7/10/2017 a Uyo jihar Akwa Ibon, na tarayyan Najeriya, na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na 2018, wanda za'ayi a kasar Rasha.
Taron wadda akeyi duk shekara ya kunshi manya manyan masu ruwa da tsaki a bangaren wasan kwallon kafa Na Najeriya, wanda suka hada da shuwagabanin NFF da sakatarorinta da mambobi 44.
Cikin mahalarta taron akwai Sakatarorin hukumar (FA) na jihohohi 36, hada da babban birnin kasar Abuja, da kuma wakilan kungiyar masu horas da ‘yan wasa na kasar da bangaren Alkalan wasannin kwallon kafa, hada da kungiyar ‘yan wasa.
Haka kuma taro ya hada da tsofin shugabannin da suka taba jagoranci hukumar ta NFF a baya, da Sakatarorin su.
Shi dai wannan taro anayinsa ne kowane shekara domin tattaunawa kan matsalolin da yake damun wasannin kwallon kafa a kasar da kuma kawo wasu abubuwa na ci gaba a bangaren wasan kwallon kafa.
Your browser doesn’t support HTML5