Kaima Ka Dara

A shirinmu na raha a wannan mako mun sami labari ne daga Usaini Uba Kachalla wanda ya bamu labarin wani Mutum da dan sa suna shan rake , sun zauna suna sha, sha suke tun suna hira, Sha dai suke ta yi har ta kai ga sun daina hira kwa ya yi shiru. Sai yaron da ya sha mai isharsa ya juyo ga uban nasa sai ya kula yana hawaye sai saboda zakin rake!.

Hmm! Sai kawai dan nan ya ce wai Baba me ya sa idan aka shuka rake tsayinsa ba ya kaiwa sama ne?, sai uban nan ya ce kai dan ubanka wannan ai sai gwamnati.