Kamaru Ta Lashe Gasar AFCON 2017 Karo Na Biyar

A wasan da akayi na cin kofin nahiyar kasashen Afirka AFCON, na shekarar dubu biyu da goma sha bakwai a kasar Gabon, jiya Lahadi 5/2/2017, an buga wasan karshe tsakanin Kungiyar kwallon kafa ta Kasar kamaru da kasar Egypt, inda kasar kamaru ta samu nasarar lashe gasar kan kasar Egypt, daci 2-1.

Tun fara wasan da minti 22, kasar Egypt, ta jefa kwallo a ragar kamaru ta kafar dan wasanta mai suna Elneny, Kamaru kuwa ta samu damar rama kwallonta ne bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 55, da fara wasan ta kafar dan wasata Nkoulou, daga bisani ana mintuna na 88, ta samu kwallon da ta bata nasara daga dan wasanta Aboubakar.

Wannan ya bata daman sake lashe kofin a karo na biyar, Bayan ta shafe shekaru goma sha biyar ba tareda ta dauki kofin ba.

Ita kuwa kasar Burkina faso, ta samu nasarar zama a matsayi na ukku ne a gasar Sakamakon doke kasar Ghana da tayi da kwallo daya mai ban haushi a wasan da sukayi a ranar Asabar a can kasar Gabon.