WASHINGTON, DC —
A shirinmu na Nishadi a yau mun sami bakunci Aminu Sharif wanda aka fi sani da Momo, wanda ya shafe shekaru ashirin ya na harkar fina finai.
Ya ce babban abinda ya fi ci musu tuwo a kwarya bai wuce matsalar satar fasaha ba, inda hakan ke dakile tattalin arzikin kasa da ma masu shirya fina-finai.
Ya kuma yi kira da Gwamnati da masu ruwa da tsaki dasu dauki tsauraran matakai wajen magance satar fasaha wanda yin haka zai taimakawa masu harkar fina finai gaya wajen tsare masu ayyukan su.
Momo ya ce akwai bukatar masu ruwa da saki da su jajirce wajen kawo karshen wannan matsala sannan su ma masu shirya fina-finai akwai bukatar samar da fasahar zamani na kulle fina-finansu wanda zai sa ya yiwa masu satar fasaha wahalar iya nadar fim din.
Wanda a cewar sa hakan ba karami taimakawa zai yi ba wajen rage masu satar fasaha da suke yiwa sana'ar su kafar ungulu.