Karin Magana Da Ya Kunshi Labari

Dr. Abdullahi Garba Imam

Shirin Harshe da Karin Magana na wannan makon zai yi duba ne akan karin magana mai bada labari, wato karin maganar da ya kunshi labari.

A makon daya gabata ne Dakta Abdullahi Garba Imam, yayi mana bayanin karin magana mai sana’a, to amma wannan satin zai tashi ne da karin magana mai labari. Inda yace shi wannan karin maganar mai labari shine irin karin maganar da mutum ba zai sanshi ba har sai mutum ya san asalin sa, kasancewar karin magana ne da fadar sa ake kawai amma ba kowa ne ya san asalinsa ba, kuma sai an san asalin sa domin ta nan ne mutum zai gane me ake nufi.

Shi dai wannan karin magana ya kasu kashi biyu, kamar yadda manazarta suka rarraba shi, na farko dai shine karin magana mai labari tsoho, na biyu kuwa shine karin magana mai labari sabo, amma baki ‘dayansu ba za’a iya cewa ga adadin su ba.

“Jifan gafiyar ‘Baidu” wannan wata karin magana ce da idan mutum bai san ta ba to ba zai taba sanin asalin ta ba, shi dai ‘Baidu wani mutum ne yaje bakin ramin gafiya domin ya kama, ya saka wuta hayaki ya fara tashi ana haka sai gafiya ‘daya ta fito da gudu ‘Baidu ya kamata ya rike mata jela, ya kuma ci gaba da hura wuta can anjima sai wata gafiyar ta kara fitowa, ‘Baidu ya dauki wannan gafiya dake hannun sa ya jefi gafiyar da ta fito, baki ‘dayan su suka runguma da gudu wato ‘Baidu yayi biyu babu. Domin sauraren cikakken missalin wannan karin magana danna sauti.