Ko Ba Komi Harkokin Tsaro Sun Inganta Inji Wasu Matasa

A yayin da wannan sabuwar gwamnati ta cika shekara guda da fara mulki, ko menene ra’ayoyin matasa akan kamun ludayin gwamnatin musamman ta fuskar tattalin arziki, da tsaro da sauran abubuwan da suke ci masu tuwo a kwarya, ta dalilin haka ne wkiliyar dandalin voa Baraka Bashir ta jiyo ra’ayoyi jama’a daban daban akan yadda suke kallon lamarin.

Da farko ta fara jin ta bakin malam Abdul’aziz Yusuf Bargoni wanda ya ce “muna iya cewa mun gamsu da yadda gwamnatin ke gudanar da ayyukanta ta wani bangaren, amma ta wani bangaren kuma gaskiya zamu iya cewa baiyi mana yadda muke tsammani ba, amma muna iya bashi uzuri domin irin halin da ya sami kasar. Idan muka duba ta bangaren harkar tsaro to lallai ya yi kokari”.

Shi kuma Ahmad Muhammad y ace “baza mu iya cewa komi ya gyaru ba kamar yadda harkokin tsaro suka gyaru wannan ma wata dama ce da koanne dan Najeriya ke al’afahari da ita sai dai kuma a daya bangarn gaskiya ana jin jiki, wato tsadar kayan abinci da sauran su”.

Talaka na cikin halin kuncin rayuwa kuma da dama ansan cewa an dade ana aikata ayyukan ashsha wadanda gyaran su zai dauki wani dan lokaci kafin a gyara.

Ga cikakken rahoton.