Wata kotu a birnin Legas ta yanke wa wani matashi Ibrahim Abu, mai shekaru 37 hukuncin daurin watannin shidda a sakamakon kama shi da laifin taba ma wata yarinya mai shekaru goma sha bakwai wadda aka sakaya sunan ta mama.
Kotun Majistire ta yanke wa Abubakar wanda ke zama a gida mai lamba 6 kusa da masallaci Isheri Olofin, a jahar Legas hukuncinne ranar juma’a da ta gabata a sakamakon laifin da kotun ta kira a matsayin cin zarafi da matashin ya-yi ma yarinyar ranar Litinitin satin da ya gabata.
Kamar yadda mujallar Vanguard ta wallafa, iyayen yarinyar sun sata koyon sana’ar gyaran gashi ne a yayin da take zaman jiran sakamakon jarawar kammala makarantar sakandire.
Rahotanni sun bayyana cewar da misalign karfe 7:30 na yamma yayin da matashin yake hanyar sa ta komawa gida Abubakar ya gamu da ita sa’annan ya taba ta ba tare da yardar ta ba a yayin da take jiran mota.
Rahotannin sun bayyana cewa matashiyar ta mare shi, yayin da shi kuma ya mayar da martani da wani falankin katakon da ke hannun sa lamarin da yayi sanadiyyar faduwar ta kasa har ta kaiga suma inda jama’a suka kai mata daukin gaggawa suka kaita asibiti.
Jami’an ‘yan sanda sun cafke Abu, wanda daga karshe aka caje shi da aikata laifin cin zarafi, a yayin da mai shari’a Osusanmi ta ce laifin ya keta sashe na 135 na dokokin jahar Legas.