Kungiyoyin Kwallon Kafa Sun Fara Kyalla Ido Domin Sayen Sababbin Zaratan 'Yan Wasa

Duk dacewa a ranar Alhamis 31 ga watan takwas 2017, aka rufe hada hadar cinikaiyar 'yan wasan kwallon kafa na duniya na shekarar 2017.
Ba za'a sake budewaba sai ranar daya gawatan janairu na shekarar 2018.

A yanzu haka kungiyoyin kwallon kafa da dama har sun fara kyalla ido wajan ganin irin 'yan wasan da zasu sayo a wannan lokacin da zarar an bude cinikaiyar a watan janairu mai zuwa.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United dake kasar Ingila ta sake nuna sha'awarta wajan ganin ta sayo dan wasan gaba na gefe dan kasar Wales, mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Gareth Bale,

A kwanakin baya ne dai kungiyar ta Manchester united, tayi tayin fam miliyan £90 ga dan wasan, sai dai mai horas da kungiyar ta Real Madrid, Zinedine Zidane, yayi watsi da batun sayarwa inda yace ba na sayarwa bane.

Sai dai daga bisani ita kungiyar ta Real Madrid, ta bukaci Manchester united da ta zo ta saye dan wasan,

Real Madrid, dai a yanzu haka tana ganin cewar tana da yan wasa irin su Marco Asensio, da Isco, da zasu taka rawar gani feye da Gareth Bale,