Me Yasa Wasu Samari Da 'yan Mata Ke Wa Juna Kwacen Saurayi Ko Budurwa?

Shirin samartaka na wannan makon ya tattauna ne da wasu matasa maza da ‘yan mata dangane da dalilan da ke sa yawancin samari da ‘yan mata ke kwace ma juna abokan hira ko na samartaka.

Da farko munji ta bakin wata budurwa wadda ta ce yawancin ‘yan mata na kwacewa abokan su samari ne saboda kwadayin abin duniya. Ta kara da cewa akwai ire iren wadannan matsalolin da dama, har ta bada misalin wata kawar ta da ta raba abokanta biyu da samarin su, kuma bata yin hakan sai dap da sun kusa aure kuma daga karshe ba auren zata yi ba.

Daga karshe ta bayyana ra’ayinta cewar bata son saurayi mai jin kanshi domin kauce wa wulakanci, ta ce tafi son saurayi dai dai da ita wanda zasu yi duk fadi tahi tare har su kaiga zama tare.

Shi kuma Adamu Muhammed Sbuwar Gandu cewa ya yi duk idan kaga haka ta faru to saurayinne ya bada kofa saboda babu yadda za’a yi haka nan kawai budurwa ta fara kokarin neman abokin saurayin ta kadashike, ba a taru an zama da yaba. Daga karshe ya ce babu yadda za’a yi ya nemi kawar budurwar sa komi kyanta.

Mujahidin Abbas ya ce lallai idan kaga saurayi ko budurwa ta komawa abokin saurayinta dama bata kaunar saurayin, haka kuma saurayi ma. Ya kara da cewa idan haka ta kasance tsakanin shi da abokin sa, lallai zai rage hulda da abokin kuma bazai iya zuwa wurin da za’a daura auren su ba.

Menene ra’ayin ku a nan?

Ku saurari cikakkiyar hirar a dandalinvoa.com