Maganganun Da Samari Da 'Yan Mata Ke Yi A Lokacin Zance

Love song

A shirin namu na yau, shirin samartaka ya ji ra'ayoyin wasu matasa maza da mata ne dangane da irin maganganun da suke yi a yayin da suke zance ko fuska da fuska ko kuma ta wayar hannu.

Yawancin samari da 'yan mata kan yi anfani da wayar su ta hannu domin zantawa da juna musamman idan yamma tayi kokuma cikin dare kamar yadda wasu suka ce shine mafi tasiri domin kuwa, akwai maganganu da dama da baza su iya duban juna ido da ido sannan su yi ta ba, amma ta wayar hannu suna iya fada ma juna duk wata magana da suka ga dama.

Menene anfani da kuma illar irin wannan soyayyar?.

Kodashike zamani ya canza, amma da alamun cewar a zamanin da ya gabata, samari da 'yan mata kan yi zance na dan gajeren lokaci ne kawai a sakamakon irin tarbiyar da iyaye suka ba 'ya'yan su, amma a wannan zamani ko da asurayi bai sami ganin budurwa ba, yana iya kiran ta a waya su dauki lokaci suna zantawa.

Ku saiurari karin bayani domin tafka muhawara a shafin mu na dandalinvoa/facebook.com