Kwanaki kadan ya ragewa wata mata mai suna Gertrude Weaver, ta zama matar da tafi kowa yawan shekaru a duniya. Matar ta mutu da shekaru 116, ranar Litinin a jihar Arkansas dake Amurka.
Weaver ta zamanto matar da tafi kowa yawan shekaru bayan rasuwar matar nan ‘yar Japan, satin daya wuce, bisa ga kungiyar bincike ta GRG dake Los Angeles, sunce an haifi Weaver a shekara ta 1898.
A satin daya wuce ne magajin garin da matar take yayi hira da ita, wanda yace mata ce mai kirki, kuma idan ka tambayeta shawarar yadda mutum zai dade a duniya sai tace, kayi amfani da man fata mai kyau, ka kyautata wa mutane, kaso makwabtanka, ka ci abincin da ka girka kada kaci abinci a gidajen sai da abinci na zamani.
Kungiyar binciken ta tabbatar da shekarun matar tayin amfani da takardun kidaya da kuma takardar ‘daurin aurenta.
Iyayen Weaver dai manoma ne kuma an haifeta a kudu maso yammacin jihar Arkansas. Satin daya wuce ne take gayawa wata ma’aikaciyar lafiya mai kula da ita, cewa tana so ta gayyaci shugaban kasar Amurka Barack Obama ranar murnar haihuwar ta mai zuwa, saboda ta zabe shi har sau biyu.