Manchester City Zata Bayar Da Kelechi Iheanacho Haya

Ana kyautata zaton kungiyar Manchester City zata bayar da hayar Kelechi Iheanacho, cikin watan Janairu na shekara mai zuwa.

Manajan Manchester City Manuel Pellegrini da wasu kungiyoyi sun yaba da kwazon matashin Kelechi Iheanacho ‘dan asalin Najeriya.

Wanda ya jefa kwallon da ta baiwa City nasara akan Crystal Palace inda aka tashi 1-0 a watan Satumba, hakane yasa ‘dan wasan ya nemi kungiyar da tayi kwaskwarimar yarjejeniyar sa da ita.

Ana ganin dai kowa na farin ciki da kwazon ‘dan wasan a Manchester City, amma yarjejeniyar sa da ita City bata kai yadda yakamata ace shi ‘dan wasan samu ba, kasancewar ya kamata ace tafi haka.

Duk da yake sai watan Janairu za’a bayar da shi, amma wasu na ganin akwai zabi gareshi, har yanzu dai Manchester bata yi masa tayin komai ba, domin sai shekara ta 2019 yarjejeniyarsa zata kare da City.