Marouane Fellaini Na Manchester United Ba Zai Taka Leda Ba

Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa na Manchester United, dan kasar Belgium, Marouane Fellaini, mai shekaru 29, da haihuwa tana iya yuwar bazai samu damar fafatawa a wasan da kungiyarsa ta Manchester zatayi tsakaninta da takwararta ta Liverpool, ba ranar Asabar 14/10/2017 a gasar Firimiya lig, wasan mako na takwas, sakamakon raunin da yasamu.

Shidai dan wasan ya samu raunin ne a wasan da kasarsa ta Belgium, tayi tsakainta da kasar Bosnia, a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na 2018 da za'ayi a kasar Rasha.

Ranar Asabar da ta gabata 7/10/2017, ne kasar Belgium tabi Bosnia, har gida ta doke ta da kwallaye 4-3, Fellani ya samu raunin ne a cikin minti na 29, da fara wasan.

A wani labarin da kasarsa ta Belgium, ta wallafa a shafinta na yanar gizo mai yuwar dan wasan zai iya shafe sati biyu yana jinyar kafarsa don haka Fellaini, bazai samu damar fafata a wasan da Kasar Belgium zatayi da kasar Cyprus, ba a ranar Talata 10/10/2017 a cigaba da fafutukar neman gurbin cin kofin kwallon kafa na duniya.

Your browser doesn’t support HTML5

Marouane Fellaini Na Manchester United Ba Zai Taka Leda Ba - 4'56"