Masu Kutse Na Sayar Da Bayanan Mutane Kan Yanar Gizo

Masu Kutse

Masu kutse kan yanar gizo ‘yan kasar Russia sun kwashewa mutane kusan Miliyan 33 inkiya wato username da mabudin password dinsu na shiga shafin sadarwa na Twitter, sun kuma yi bajakolinsu kan yanar gizo.

An gano satar bayanan ne bayan da akayiwa shugaban Facebook Mark Zuckerberg kutse a shafinsa na Twitter, ita ma shahararriyar mawakiyar nan Katy Perry anyiwa nata shafin kutse.

Sai dai kuma kamfanin Twitter ya musanta cewar anyiwa runbun ajiye bayanansa kutse, amma kuma ana dubawa a gani ko akwai wata kofa da aka shiga aka samo bayanan.

Miliyoyin bayanan da aka saka a yanar gizo domin sayarwa ana tunanin sun fito ne daga masu kutsen da suka balla shafin Myspace da Linkedin, cikin bayanan kuwa akwai wadanda aka sace tun shekarar 2011.

Mutane da yawa na anfani da mabudin password dinsu a duk shafinansu na yanar gizo ba tare da suna canzawa ba, wanda hakan zai iya taimakawa ayi musu kutse cikin sauki. An gano cewa cikin makon da ya gabata anyiwa fitattun mutane kutse akan shafinsu.