Matasa...Zaku Iya Auren Budurwa Mara Ilimi da Aikin Yi Ko Sana'a?

A wannan makon, mun sami zantawa ne da wasu samari domin jin ra’ayoyin su akan aure, tambayar tamu kuma itace; zaka iya auren budurwar da bata da ilimin boko, bata sana’a ko wani aiki?

Mun ji ta bakin matasa da dama, koda shike babu yadda za’ayi dukkan ra’ayoyin su zama daya, amma da dama sun nuna cewar lallai so na ainihi bashi da alaka da aikin yi.

A cewar matashi Abba Ibrahim, auren mace maras ilimi ko aikin yi, ya dogara ne a kan wasu dalilai. Saurayin ya kara da cewa zai iya auren ta idan tana da kyau sai daga baya ya sata a makaranta har ta sami ilimin bayan sun yi aure.

Shi kuma Abubakar Nasir Yusuf cewa yayi babu shakka zai iya auren mace maras ilimi domin kuwa a nasa ra’ayin, idan yana aiki, matarsa na aiki babu yadda za’a ayi su sami lokacin kula da yaran su, dan haka ya gwammace ya auri wadda zata zauna gida ta kula da yara.

Abdul’azizi Aliyu kuma cewa yayi ba zai iya auren wadda bata da aikin yi ko sana’a ba, domi a cewar sa zata dauke maka wasu larurorin kuma idan suka hada kai zasu ciyar da iyalin su gaba. Daga karshe ya ce farar mace fa ba abar yaddawa bace komin rashin ilimin.

Saurari cikakkiyar hirar a nan…dandalinvoa.com