An bukaci Maniyyata aikin Hajjin bana daga jihar Lagos, dasu kasance jakadu na kwarai ga jihar ta Lagos da kuma Najeriya baki daya, da kuma gudanar da adu’oin samun zaman lafiya da ci gaban kasa.
Gwamna jihar Akinwumi Ambode, ne ya bayyana haka alokacin yakewa maniyyatan jawabi a sansanin su a birnin Lagos.
A ranar 23, ga wannan wata ne za’a fara jigilar maniyyata Najeriya zuwa kasar Saudia, inda jihar Lagos ke da dubu ukku da arba’in da bakwai daga cikin fiye da dubu 66.
Maniyyatan sun yaba da kokarin Gwamnatin jihar Lagos,wajen tabbatar da ganin cewa sun gudanar da aiyukan su na ibadah cikin sauki.
Wani maniyanci da wakilin muryar Amurka, yayi hira dashi mai suna Hussain Wasiu, yace tabas wannan karon an fara harkokin akan lokaci kuma an bamu harami na sawa da kuma Raguna.
Wata maniyaciya mai suna Bolade, tace an shirya tsaf duk da dai ba za’a rasa wasu ‘yan tangrada nan da can ba, amma Alhamdulillahi idan aka kwatanta da na baya.
Ta ce suna fatan samun wadanda zasu sasu akan kyakkyawan tafaki wajen aikin Ibadah, a kasa mai tsarki kuma muna fatan zasu taimakamana ta yadda ba zamu sha wuya ba.