Mutane 135 Aka Tabbatar Ebola Ta Kashe A Afirka Ta Yamma - 17/4/2014

Ma'aikatan kiwon ladfiya a kofar wani dakin da aka kebe masu fama da cutar Ebola a Conakry, babban birnin kasar Guinea.

Hukumar Kiwon lafiya ta Duniya, WHO, ta ce yawan mutanen da suka mutu a dalilin barkewar annobar cutar Ebola a Afirka ta yamma ya karu zuwa akalla 135.

A cikin wata sanarwar da ta bayar yau alhamis, hukumar ta ce ma’aikatar kiwon lafiya ta Guinea ta bada rahoton cewa mutane 122 suka mutu, yayin da jami’an kiwon lafiya na Liberiya suka ce mutane 13 suka mutu a kasarsu.

Hukumar WHO ta ce jami’ai su na binciken mutane fiye da 200 wadanda aka tabbatar ko kuma ake kyautata zaton su na dauke da wannan cuta ta Ebola a kasashen Guinea, Liberiya da kuma Saliyo.

Wasu mutane 6 da aka yi zaton sun kamu da wannan cuta ce a kasar Mali an bincika an gano cewa ba ita ce ba.