WASHINGTON, DC —
Wasu 'yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne, sun kai farmaki kan garin Chibok dake yankin kudancin Jihar Borno a cikin daren litinin, inda suka kona gidaje da makarantu da kantuna, sannan suka sace dalibai da aka ce yawansu ya kai 200, dukkansu mata, suka shiga daji da su.
Mazauna garin na Chibok sun shaida ma sashen Hausa cewa 'yan bindigar sun wkashi wadannan mata a cikin wasu manyan motocin da suka kai harin da su, kuma wannan ba shi ne karon farko da suek kai hari kan garin ba.
Haka kuma an ce wakwai wasu daliban mata da suka samu nasarar tserewa ma 'yan bindigar suka shiga daji, kuma ana ci ga ba da nemansu yanzu haka.