Na'urar Tantance Katin Zabe Ko Yin Magudi

Yayinda ake ta shirye shiryen babban zabe dake tafe ranar 28 ga wannan watan, wasu matasa sun bayyana ra’ayoyin su akan na’urar nan ta tantance katin zabe. Abinda wasu jam’iyyu goma da ‘yan takarar shugaban kasa biyar suka ce basu yi yarda da ita ba.

Malam Zakari Ya’u Adamu ya fadi cewa wannan na’urar ta tantance katin zabe wani sabon abu ne da aka kawo amma da wata manufa ta daban.

A ganin malam Zakari, gwamnatin tarayya ta kawo wannan na’urar ne don son kanta, don kuma yin magudin zabe saboda yadda aka tsara katin, don da zarar katin ya sami ‘yar matsala, bashi kuma da sauran amfani. Malam Zakari ya kuma goyi bayan jam’iyyu da ‘yan takara da suka ce basu amince da wannan na’urar ba.

Shi kuma Malam Hamisu Adamu cewa yayi, kawo na’urar tantance katin zabe da hukumar zabe tayi zai yi amfani sosai, ya kuma ce akwai tabbacin na’urar zata kawas da magudin zabe in Allah Ya yarda.

Game da jam’iyyu da ‘yan takarar da ke jayayya da yin amfani da wannan na’urarar kuma, Malam Hamisu cewa yayi “ a ganin sa duk shiri ne na ‘yan Jam’iyyar PDP”.

Kamar yadda zaku ji a nan, ga cikakkiyar hirar wadannan matasan da wakiliyar Dandalin VOA.