NDLEA Ta Cafke Miyagun Kwayoyi Fiye Da Kilo Miliyan Da Dari Uku

Miyagun Kwayoyi

Hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi NDLEA ta jihar Gombe ta bayyana cewa ta kame mutane 94 ta kuma karbe kilo 1,330.137 na muyagun kwayoyi a shekarar 2017. Kwammandan hukumar na jihar Gombe, Mr. Aliyu Adole ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a jihar ta Gombe.

Yace a cikin mutane 94 da aka damke an yankewa 48 hukunci sauran kuma na jiran shara'a, a tsakanin wannan lokacin an hana miyagun kwayoyi kilogram 1,330.137 shiga kasuwa wanda kilo 498.244 we-we ne, sun kuma kame wani matashi wanda ke saida cocaine a cikin jihar ta Gombe da kilo 14.8 na cocaine din.

Baya ga haka akwai wani hadi da ake yin da ake saidawa mutane, wanda ake kira madarar Sukudaye shima an kame kimanin duro 7, a cewar Adole.

Kwamandan ya kara da cewa a Disambar 2017, hukumar ta kama wani tsoho da we-we mai nauyin kilo 32 akan titin dukku zuwa Bajoga akan hanyar shi ta zuwa saida ita.

Adole yayi kira ga iyaye da su lura irin mutanen da ‘ya’yansu ke mu’amulla da saboda gujewa mu'amulla da mugayen mutane.