WASHINGTON D.C —
A shirinmu na nishadi na yau na mussamam ne domin kuwa mun sami bakuncin Maryam Said Bala wacce aka fi sani da Maryam Tarbiya Bauchi
Maryam Tarbiya ta ce a iya sanin ta , ta fara son waka da rera ta tun bata bada ma’ana har ta zo tana yin masu ma’ana
Tarbiyar dai ta fi raja’a ne da wakokin soyayya ko na siyasa amma wasu lokutan takan rera wakar fina-finai
Ta ce babban kalubalen da mawakan arewa ke fuskanta shine na rashin damawa da su a harkokin cigaban kasa, tare da rashin basu muhimmanci a cikin alumma
A fannin tsegumi kuwa a gobe ne za’a gudanar da wani gagarumin bikin karrama mawakan Kannywood bisa jagorancin Inuwar Fasaha … ku biyo mu domin jin cikakken shirin.