WASHINGTON D.C —
A yau mun sami bakuncin wani mawaki Salisu Babba wanda aka fi sani da Salisun Fati mawaki da ya shafe shekaru yana harkar waka, inda ya bayyana mana cewar wakarsa ta Fati ce ta samar masa lambobin yabo.
Mawakin ya bayyana cewa ya fara waka ne tun daga islamiyya, kuma yana wakokin fina finai da kuma soyayya, ya kuma kara da cewa yana matukar shi'awar sana'ar sa kuma ya yi imanin cewa baiwa ce daga Allah.
Daga karshe ya yi karin bayani akan dalilan da suka sa ya rera wakar Fati wadda ta yi suna sosai a matsayin tamkar bakandamiyar sa, domin kuwa a cewar sa Allah ne bai nufa ba amma da yanzu Fati ce abokiyar zaman sa.
ku biyo mu domin jin cikakkiyar hirar da shi.