Ra'ayoyin Iyaye A kan Soyayyar 'Ya 'Yan Su

Iyaye mata, wadanda suka hallarci tattaunawa akan cutar Polio da Jummai Ali. Mayu 13, 2013

A ci gaba da tattaunawar mu akan mizanin shekarun da ya kamata iyaye su bar 'ya'yan su su fara soyayya, wasu iyaye sun tofa albarkacin bakin su da kuma hangen da suke wa lamarin.

A cewar malam Inusa Gibson daga gandun albasa Kano municipal, ya kamata daga shekaru goma sha shidda zuwa goma sha bakwai, saboda a ganinsa lokacin balaga kenan kuma a cewar sa ya kamata iyaye su kula da yaran su domin sanin gidan da ya kamata su je domin neman aure.

Malamin ya ba iyaye shawarar cewa su rika kai zuciya nesa musamman dangane da aurar da 'ya'ya mata, a bar su, su sami ilimin jami'a kafin a aurarr da su. hakan a cewar sa zai taimaka wa ma'auratan samun saukin rayuwa.

Shi kuma Malam Nura shi'aibu cewa ya yi soyayya ta danganta da iyaye ko gida, ya kara da cewa kamar yadda ya sani a zamanin su ba su zuwa zance sai dai idan iyaye sun lura da hankalin yaro sai su nemi izinin iyayen domin hada masu aure.

sa'ido akan yara abu ne mai muhimmanci, kuma ya kamata iyaye su rika duba wayar wayar 'ya'yan su domin kaucewa yaudarar matasa. ya kara da cewa hatta makarantar su ya kamata iyaye na zuwa ganin su da kuma tambayar makarantar irin rayuwar da yaran ke ciki.

Da muka juya bangaren iyaye mata kuma, ya kamata iyaye su bar 'ya'yan su mata su kai wani matakin karatu a jami'a tukuna kafin a bar su su fara soyayya, kuma a cewar ta bai kamata iyaye su ba 'ya'yan su wayar hannu ba har sai sun kai shekaru akalla ashirin da biyar.

Daga karshe malamar ta yi kira ga dukkan iyaye da su rika lura da irin rayuwar da 'ya'yan su suke zama, su kuma sakar masu jiki domin kaucewa moye masu wasu maganganun sirri.