Real Madrid Zata Kece Raini Da Atletico Madrid A Gasar (UCL)2016/17 Semi-Final

A jiya an fafata a gasar cin kofin Nahiyar Turai mai taken Europa League, 2016/2017 a matakin wasan kusa da na kusa dana karshe Quarter Final, karawa ta biyu kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, ta doke Anderlech, da ci 2-1, Schalke 04 nada 3 Ajax nada 2.

Besiktas ta sha Lyon 2-1 daga bisani aka buga bugun daga kai sai mai tsaron gida, Lyon, ta samu nasara 7-6, Genk ta yi kunnen doki 1-1. Bayan kammala wasan an fidda jaddawalin kungiyoyin da zasu fafata a tsakaninsu a zagaye na gaba wato Semi Final.
Celta Vigo, da Manchester United, sai Ajax da Lyon, za'a buga wasan ranar Alhamis 4 ga watan Mayu 2017 a matakin zagaye na farko sai ranar 11/5/2017 a dawo zagaye na biyu.

A bangare gasar cin kofin zakarun nahiyar turai (UCL)2016/17 an fitar da nata jaddawalin na Semi-Final domin neman zuwa wasan karshe na Uefa 2016/17
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da Atletico Madrid, ranar Talata 2/5/2017
Monaco da Juventus ranar Laraba 3/5/2017.

Your browser doesn’t support HTML5

Real Madrid Zata Kece Raini Da Atletico Madrid A Gasar (UCL)2016/17 Semi-Final