Sabuwar Hanyar Aikawa Da Sako Mai Suna ‘Allo’ Daga Google

Google na shirin fitar da wata sabuwar hanyar aikawa da sakonni mai suna Allo, kamfanin dai ya kawata Allo ta hanyar da zai maye gurbin karfar aika sakon karta kwana ta Hungout.

Allo zai kunshi duk abubuwan dake cikin fitattun hanyoyin aika sako kamar su Hangout da WhatsApp. Google zai kawata wannan sabuwar kafa da fasahar nan ta Google assistance da smart reply.

Ita dai fasahar Google assistance za a iya amfani da ita wajen samo bayanai da ake nema. Smart reply kuwa sabuwar fasaha ce da duk lokacin da aka aiko da sako musamman wanda ya kunshi hoto, fasahar zata mayar da amsa missali idan aka aika da hotan abinci, smart reply zai gane abinci ne zai kuma aika da amsa kamar “Abincin zai yi dadi” amma duk da turanci.

Kamfanin Google dai yace zai fitar da wannan sabuwar fasaha nan bada dadewa ba, mutane zasu iya sauketa kan wayoyinsu na Android da ios ba tare da sun biya ko sisin kwabo ba.