Wannan dai shine karo na uku da gwamnatin Najeriya ta kawo sababbin tsare tsare ko manufofi a bangaren musayar kudaden kasashen ketare cikin kasa da shekara guda.
Mataki na farko da gwamnatin ta dauka shine tsarin tsayar da sayar da dala ga kamfanonin canji kokuma ‘yan canji, ta mayar da komi a hannun bankuna, daga bisani kuma ta hana su kansu bankunan yayin da ta mayar da komi a hannun babban bankin kasar wato CBN.
Sai dai kuma a halin da ake ciki yanzu gwamnatin ta sake tunani, domin kuwa ta bullo da sabuwar manufar tsame hannun bankin inda tace kasuwa ce zata yi halinta wajan tsayar da farashin dalar amma ta hannun wasu bankuna bakwai data zaba.
Wannan sabon tsari ya fara aiki ne daga ranar litini 21 ga watan Yulin da muke ciki, sai dai hakan ya jefa fargaba a zukatan ‘yan kasuwa da masu harkar musayar kudade a kasar.
Saurari Cikakken Rahoton A Nan.
Your browser doesn’t support HTML5