Babban kocin kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekaru 23 Samson Siasia ya ce ya godewa Allah domin sa’ar da ‘yan wasan sa suka samu wajan doke abokan karawar su na Senegal a gasar shiga wasan cin kofin Olympic da za’a buga a shekara mai zuwa idan Allah ya kai mu.
Kocin ya kara da cewa yana mai matukar godiya da farin ciki musamman ganin irin rawar da mai tsaron gidan ‘yan wasan na Najeriya Emmanuel Daniel ya taka a lokacin wasan.
Kungiyar ‘yan wasan ta Najeriya dai ta doke abokiyar karawar ta ne da ci 1 – 0 a jiya laraba a wasan su na kusa da na karshe wanda zai basu damar karawa da ‘yan wasan Algeria.
Dan tsaron gidan na Najeriya ya nuna bajintar sa ne wajan tare kwallon bugun daga kai sai mai tsaron gida da ‘yan wasan na Senegal suka samu, wanda daga bisani ‘yan wasan na Najeriya suka sami nasara bisa takwarorin nasu har wasn ya kai karshe.
Samsin Siasia ya ce “Emmanuel Daniel ya taka rawar gani kwarai da gaske musamman yadda ya damke kwallon da ‘yan wasan Senegal sukai yunkurin jefa mana a raga, ya kuma kara da cewa lallai Allah yana tare da mu, domin kuwa ‘yan wasan Senegal sun kai mana farmaki da dama amma Allah yak are mu”.
Kocin ya ce “samar da damar jefa kwallo a raga daban yake da jefa kwallon a raga, domin kuwa mun riga mun sami nasara, dan haka ban damu da cewar mun bar ‘yan wasan na Senegal suka yi yadda suke so ba.
Daga karshe kocin ya ce yana mai matukar farin cikin samun wannan damar ta sake doke Senegal kamar yadda suka sami galaba akan su a wasan cin kofin Afirka da aka buga a shekarar 1992.