WASHINGTON, DC —
Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin sace daruruwan dalibai mata da aka yi a watan da ya shige a garin chibok na Jihar Borno. Har ila yau kungiyar ta yi barazanar cewa zata sayar da su.
Wannan ikirarin yana kunshe cikin wani faifan bidiyon da kungiyar ta ba ‘yan jarida yau litinin. A cikin bidiyon, shugaban kungiyar, Abubakar Shekau, ya ce “ni na sace ‘yanmatanku" ya kuma lashi takobin sayar da su a kasuwa.
Wani mahaifin da aka sace masa diya ya fadawa VOA cewa su kam sun rasa nayi sai dai su ci gaba da yin addu’a da azumi ko Allah zai kubutar musu da ‘ya’ya.
A jiya lahadi, shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya umurci manyan jami’an tsaro da su yi duk bakin kokarinsu wajen kwato wadannan dalibai mata. Shugaban yayi alkawarin cewa duk inda wadannan mata suke, za a kwato su