Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da tabbaci ga ‘yan wasan Golden Eaglets da suka fara lashe gasar FIFA ta cin kofin duniya a matakin ‘yan kasa da shekaru 16 a wancan lokacin, da cewa zai cika musu alkawuran da ya musu shekaru 30 da suka gabata.
Babban mai baiwa shugaban shawara kan harkokin manema labarai, Garba Shehu, ya fada a wata sanarwa cewa an gabatar da wannan bukata a gaban shugaban.
A cewar Shehu, ba a cika umurnin da shugaba Buhari ya bayar ba ne a wancan lokacin.
Gasar dai ana yin ta ne yanzu a matakin ‘yan kasa da shekaru 17, wacce Najeriya ta lashe a karo na biyar bayan da ta doke kasar Mali da ci 2-0.
Najeriyar ce kuma ta fara daukan kofin gasar a shekarar 1985 wadda China ta dauki bakunci, bayan da ta doke West Germany itama da ci 2-0 a wasan karshe.
Tawagar ‘yan wasan a wancan lokacin ta kasance a karkashin jagorancin dan wasan Najeriya Nduka Ugbade, wanda shi ne mataimakin mai horar da ‘yan wasan Flying Eagles na yanzu.
Sanarwar dai ta nuna cewa abin takaici a ce kantomomin jihohi ba su cika umurnin da aka basu na karrama ‘yan wasan ba a wancan lokacin, tana mai nuni da cewa ita gwamnatin tarayya tuni ta cika nata alkawuran.