Hukumar kwallaon kafa ta Najeriya (NFF) zata yi jawabi cikin wasu kwanaki agame da Stephen Keshi, a cewar shugaban kungiyar Amaju Pinnick, a yayin da ya bayyana a gaban kwamitin da ke kula da kwallon kafa na majalisar dattawan Najeriya wajan yin kasafin kudi na shekarar 2015.
Keshi na da wa’adin zuwa nan da 12 ga watan Maris, ya yanke hukucin ko yana so ya sake sabunta yarjejeniyar kwangilar da hukumar NFF ta bashi ko ya tafi inda yafi mashi.
Shugaban na NFF ya yi bayanin cewa jinkirin da aka samu na da nasaba da kokarin kaucema maimaita kuskuren da aka samu a baya wajan daukar kocin manyan kulob aiki.
A cewar shugaban na NFF “lokacin da aka zabe ni shugaban wannan hukumar, na duba takardun daftarin daukar Koch Koch aiki da dama da akayi a da, anyi ne ba tare da an fayyace wasu abubuwa da dama ba.
Dan haka na yi wani zama na musamman da duk wani kwamitin da ke da alhaki wajan daukar Koch aiki daga kwamitin kwararu masu kula da fannin shari’a na tarayya da sauran kwamitoci, dan gudun tasowar wasu abubuwa daban bayan daukar Koch aiki.