Ta Jefa 'Ya'Yan Kishiya A Cikin Rijiya

Rundunar ‘yan Sandan jihar Nasarawa ta damke wata mata mai suna Aisha Isa, a bisa zargin cewa ta jefa ‘ya’yan kishirarta su biyu cikin rijiya wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar yaran a Yelwa Bassa, dake karamar hukumar Kokona a jihar Nasarawa.

Yaran Zainab, mai shekaru hudu da Ramatu, mai shekaru biyu, a cewar rahotun Aisha, ta daure hannayensu da kafafuwarsu kafin ta jefa su cikin rijiyar.

Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Mohammed Kura, wanda ya tabbatar da mummunar labarin ya ce yanzu haka tana hannun jami’an tsaro masu bincike.

Ya ce Aisha, mai shekaru ashirin (20) da take amsa laifinta ga jami’an ‘yan Sanda, tace ta aikata aika aikan ne saboda mahaifiyar yaran tahana su zuwa mata aike.

Daga bisa ta nuna takaicin akan abinda ta yi, ta kuma nemi a yimata afuwa tana maicewa da yi dana sani wannan ta’azar data aikata.