Vincent Enyeama Bazai Buga Wasan Super Eagle Da Afika ta Kudu Ba

Nigeria's goalkeeper Vincent Enyeama seems to defy gravity in the net for Nigeria at the Brasilia national stadium in Brasilia, June 30, 2014.

Kaftin ‘din kungiyar kwallon kafar Super Eagle ta Najeriya, Vincent Enyeama, baya cikin ‘yan wasan da zasu buga wasan ‘kawancen da kasar Afirka ta Kudu, saboda matsalar ciwon baya da yake fama da ita.

Shi dai mai tsaron ragar Super Eagles, ya samu buga wa Najeriya wasanni har sau ‘dari, a nasarar da suka samu ranar Laraba, kan kasar Uganda, inda aka tashi 1 – 0, amma ba zai sami damar shiga wasan da zasu buga da kungiyar Bafana Bafana ba.

Wannan yana nufin Enyeama, ba zai samu damar zama ‘dan wasan Super Eagles daya fi kowa yin wasannin kungiyar ba, yayi dai kunnen doki da tsohon kaftin Joseph Yobo a yin wasani har sau ‘dari.

Duk da haka dai shine ‘dan Afirka na hudu mai tsaron gida da ya yi wa kasar wasanni ko gasa masu yawa, bayan mutane uku ‘yan kasar Masar, wanda suka hada da Essam El-Hadary, Nader El-Sayed da Ahmed Shobair.