Wani Dan Kallo Ya Ketara Cikin Filin Wasa Tsakanin Turkiya Da Koroshiya

Wani abu da ya girgiza jama’a a wasannin nahiyar turai da ke wakana yanzu haka a kasar Faransa shine yayin da ake karawa tsakanin Turkiyya da Koroshiya, kasar Koroshiya ta sami Nasarar jefa kwallo guda sai kawai aka ga wani mutum daga cikin ‘yan kallo ya ketara cikin filin wasan inda ya rungume su a lokacin da suke murnar jefa kwallon.

Wannan lamari dai yasa jama’a da dama ma’abota sha’anin tsaro sun tofa albarkacin bakin su da kuma kira da wadanda abin ya shafa da su kiyaye kwarai domin inda wannan dan kallon yazo da mummunar aniya da anzo karshen wasan Euro Kenan.

Wannan kuma ya zo dai dai da lokacin da hukumar kwallonkafa ta Turai ta ci kasar Rasha tarar kudi Euro 170,000. Bayan tashin hankalin da ‘yan kallo daga kasar ta Rasha da ingila suka yi a lokacin da suke kallon karawar farko wadda aka tashi da ci daya da daya.

Wannan lamari ya ja hankalin hukumomin kasar Rasha musamman ganin yadda kasar ke shirin karbar bakuncin wannan gasa ta wasannin kwallon kafa da za’a gudanar a shekarar 2018, hukumar Turai ta yi wa kasashen biyu kashedin cewa su ja kunnuwan masu goyon bayan ‘yan wasan su, da kuma yi masu barazar cewa da zarar an sake samun wani tashin hankali makamancin wannan to lallai zau koma gida kuma karshen wasansu kenan.

Wani abin mamaki dake wakana kuma shine a wasan da za’a buga tsakanin kasar Faransa da Albeniya a ranar laraba idan Allah ya kaimu, masu canke sun nuna cewa kasar Albeniya ce zata yi nasara amma ba’a san maci tuwo ba sai miya ta kare.

Sa’annan a wasannin KOPA America da ake ci gaba da gudanarwa kasar Brazil ya ti bankwana bayan kashin data sha daga hannun Peru da ci daya da babu, wanda yasa kasar ta Brazil shiga wani mummunan tarihi na kasancewa a cikin shekaru talatin wannan shine karo na farko da aka jefar da ita a zagaye na farko a babban wasa irin wannan.

Ga cikakken rahoton.