Yayi Harbi Sau 83 Kan Barawo Bai Same Shi Ba, Sai A Na 84

Aikin dan sanda ba karamin aiki bane, amma duk da haka akwai wani sashin ko bangaren aikin da bashi da wahalara aikatawa, a misali harbin mai laifi. bai kamata a ce kwararren dan sanda ya yi harbi sau tamanin da hudu ba sa'annan ya sami abin da ya ke hari.

Ranar juma'ar da ta gabata ne wani dan sanda a birnin New York ya yi arangama da wani matashi mai shekaru ashirin da bakwai da haihuwa mai suna Jerrol Harris a lokacin da yake kokarin sace motar wani mutum kuma ya budewa dan sandan wuta da bindiga.

'Yan sandan sun bi matashin a guje bayan harbin da yaron ya yi masu, amma daga karshe suka samu suka kama shi bayan da wani daga cikin su yayi har dai-dai har sau tamanin ta uku amma sai a na tamanin da hudu sannan ya yi dace har ya sami matashin a kafada.

Bincike ya nuna cewar matashin tsohon mai laifi ne, na farko an taba daure shi a sakamakon zargin sa da aka yi da aikata fashi da makami, bayan haka kuma an taba kama shi da laifin mallakar makami ba tare da izini ba.