Wani Matashi Ya Zuba Guba A Gidan Sayar Da Abinci A Jihar Cross River

Wani al’amari da ke ci gaba da girgiza hankulan jama’a a jihar Cross River, dake yankin Niger Delta, shine yadda ake zargin wani mutum mai gidan abinci ya zuba guba a abincin da yake sayarwa, lamarin da ya yi sanadiyyar rayukan wani miji da mata, da kuma haifar da mummunar illa ga wasu mutane 46.

Wannan lamari ya yi matukar daurewa mutane kai, wanda ya kaiga tunzura jama’ar karamar hukumar Ogoja, inda gidan abincin yake har suka yi yunkurin hallaka shi amma jami’an ‘yan sanda suka kwace shi suka kuma yi awon gaba da shi zuwa babban ofishinsu dake Calabar.

Domin jin halin da ake ciki na faruwar wannan aika-aika, wakilin sashen Hausa na muryar Amurka, Lamido Abubakar Sokoto, ya ji ta bakin kwaminshinan rundunar ‘yan sandan jihar Alhaji Hafiz Muhammad Inuwa, wanda ya bayyana cewa;

“A halin yanzu muna kan bincike akan mutumin da ake zargi da amfani da guba cikin abincin da yake sayarwa jama’a, koda shike bincike ya nuna mana cewa wata na biyu Kenan da aka koreshi daga yankin saboda ya addabi jama’a da ‘yan sace sace, da aikata laifuka”

Kwamishinan, ya kara da cewa kawo yanzu asibitin da aka kwantar da mutanen da suk ci abincin ta salami mutane 44, da aka kwantar sakamakon rashin lafiyar da suka kamu da ita a dalilin cin abincin, saura mutum biyu dake kwance kuma likitocin basu kammala tantance lafiyarsu ba.

Bayyanar jami’an tsaro a yankin na Ogoja, ya kwantar da tarzomar da jama’ar yankin suka yi yunkurin tayarwa wadda ka iya sanadiyyar rayuka da dukiyoyin jama’a.

Mai ba gwamnan jihar shawara akan harkokin baki mazauna jihar Hon, Musa Maigoro, ya bayyana cewa hukuma ta ladabtar da matashin a sakamakon bata yaran da yake yi, shine ya ce zai dauki fansa.

Lamido Abubakar Sokoto nada Karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Wani Matashi Ya Zuba Guba A Gidan Sayar Da Abinci A Jihar Cross River