Wankan Swagger Burgewa - In ji 'Yan Mata

Swagger

Wankar Swagger, sabuwar shigar da 'yan mata ke yayi , domin burge samari da kuma shiga tsara. Mafi yawan 'yan Mata dai sun ce duk budurwar da ta amsa sunanta cikakkiyar mace, ita ke shigar Wankar Swagger

Ko mecece Wankar Swagger?

“Asma'u Muhammad cewa ta yi ta na Wankar Swagger ne domin ta cika cikakkiyar budurwa ta kuma amsa sunanta. Ta kara da cewa, "ina wannan wanka ce ta swagger saboda ta saje da zamani ta kuma yi kasuwa wajen samun saurayi mai kudi." A cewarta muddin ba ka yi wankar swagger ba, budurwa ba ta samun saurayin da ya isa sai dai ta sami lami! Hakan ne ma ya sa ya zamo wajibi tayi wankar swagger “

Ita kuwa Nafisa Lawal Ibrahim cewa ta yi “ina wankar swagger ta hanyar sanya tufafin zamani irinsu wando wanda ake ce masa Pencil trouser da Boyfriend jacket sai mayafi Burberry bayan ta sanya abin daure gashi wato acuci maza domin ta fito fes ta yi kasuwa

Wata uwa da muka zanta da ita Aisha Muhmud Bello cewa ta yi“wannan ba dabi’a ce da za ta haifar da Da mai ido ba , mussamam ma ga al’ummar Malam bahaushe da aka san yan Mata da kunya da kamala da mutunci wanda shi ake dubawa da zarar an zo neman aure, sai gas hi wannan dabi’a ta canza inda yan mata ba su gane muhimmanci shiga ta kamala ba inda wasu iyaye mata ke mara wa yaransu baya wajen sanya matsatssun kaya.