Wasanni Hanya Ce ta Karfafawa Matasa Dogaro Da Kai

Somali Sports

Wasanni na daya daga cikin al’amuran da ke samar wa matasa madogara, musammam a kasashe irin Najeriya, dake fuskantar matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa. Ko bayan ga sha’anin motsa jiki da samar da hadin kai dakuma kawar da hankulan matasan daga shiga lamuran ashsha.

Wasanni dai kan kasance wata dama ta karuwar tattalin arziki, dalili kenan da yasa wasu masanan ke ganin cewar wasanni babbar hanya ce ta karfafawa matasa dogaro da kai musammam ga gwamnatoci da hukumomin bada tallafi dama ‘dai ‘dai kun jama’a.

Wakilin mu Murtala Faruk, ya ziyarci filin wasanni na Sokoto, inda ya tarar da ‘daruruwan matasa dake taruwa da yammacin kowacce rana domin gudanar da wasanni iri dabam dabam. Yakuma sami damar zantawa da wani matashi mai buga wasan raga, matashin dai ya bayyanawa Murtala, cewa wannan wasan shi kadai ne madogara a gurunsa, domin kuwa a dalilin sane ya sami matsayin da yake a kai halin yanzu, wanda shine Koch yana kuma koyar da wannan wasa ga mutane da dama, hakan shine sana’ar sa domin bashi da wani abun da yafi wannan wasa a duniyar nan.

Matashin dai yayi kira ga gwamnati da ta taimakawa harkokin wasanni, domin wasanni nada matukar amfani a wannan zamani.